A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, ga abin da Shahidin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatullah al-Uzma Shahid Sayyid Ali Khamenei, ya faɗa game da matsayin Yahudawa bayan ’yantar da Falasɗin.
Ya ce: “Akwai wasu mutane a duniya, waɗanda suke magana a matsayin wakilan duniya, suna yi wa matsayar Jamhuriyar Musulunci game da Falasɗin ƙarya. Suna cewa wai Iran ta yarda cewa Yahudawa ko ’yan Sahyoniya ya kamata a jefa su cikin teku! Wannan ƙarya ce. Wani lokaci a da wasu daga cikin Larabawa sun yi irin wannan magana, amma mu ba mu taɓa faɗa ba. Ba mu jefa kowa cikin teku.
Muhimmin abu shi ne ra’ayin jama’a da ra’ayin gwamnatin da za a kafa bisa zaɓin mutanen Falasɗin.
Su ne za su yanke hukunci game da mutanen da suke a wannan ƙasa.Akwai yiwuwar watakila su ce duk su zauna a Falasɗin, hakan yana yiwuwa.
Kamar yadda ya taɓa faruwa a wasu ƙasashen Afirka lokacin da na je a lokacin da nake shugaban ƙasa: sun yi gwagwarmaya suka yi nasara suka kori Turawan Ingila da suka mamaye su. Amma daga ƙarshe sai suka bar waɗannan Turawan a ƙasarsu, suka ga hakan ya fi masu amfani.
Haka ma mutanen Falasɗin — watakila su ga ya dace su bar su su zauna, ko kuma su ce a tafi da wasu daga cikinsu, ko dukkaninsu. Zaɓi yana hannunsu. Mu ba mu da wani ra’ayi da muke tilasta wa kowa a wannan batu.”
Ra'ayinka